Tuesday, June 17, 2008

Hajji dai Farko

Tambaya:

Ni Babban ma'aikaci ne kuma me tarbiyya, Alhamdu Lillah Bani da gidana nakaina, ina haya ne, kuma ina da kudin da baze isheni sayen gida ba amma ze ishe ni yin aikin Hajji. shin zan sauke faralin Hajji ne tareda cewa ina haya? shin kuma ya halarta agareni da in jinkirta yin Hajjin har se nase gida, tare da cewa wannan hakan ze dauki shekaru masu yawa?

Daga: Shafin: www.islamtoday.com/questions

Malami me Amsa:
Al'allama Ustaz Dr. Abdullahi bn mahfuuz bn biih, tsohon Ministan ma'aikatan Shari'a ta kasar Mauritania.

Rana:
01-12-1428 A.H.
Amsa:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Manzan Allah. bayan haka Wajibine gareka yakai dan'uwa da kaga batar da wajabcin Hajji, domin shi wajibine da baayin jinkiri a cikinsa, kamar yanda da yawa daga cikin Malamai suka tafi akai, to tunda kanada kudi daze ishekan yin aikin Hajji, kuma bazaka bar iyalanka ba a cikin kunci, toyazama dole akanka katafi kayi aikin Hajji kada ka jinkirta shi, domin Hajji wajibi ne, wanda ba'a jinkirta shi, kasmar yanda Imamu Malik da Imamu Ahmad suka tafi akan haka, kuma zance ne me k'arfi a wajen Hanafiyya.

HUKUNCIN YIN LAYYA BA'A GARI NA BA


TAMBAYA:

Mu muna zaune a wani Gari, kuma Mahaifiyata da Y'an Uwana suna yanka wani adadi na Layya a kowace shekara, Ni kuma inaso in aikawa da Kawuna da kudin abin Layya na , don yasaya yayi min yankan, saboda halin talauci da suke a ciki, kuma shi kawuna yana zaune a wani gari ne da ban, shin ko zaku bani shawara gameda haka, koko inyi layya na a garin danake zaune, kuma wanne ne yafi falala? tunda ni zan wakilta wani ne da yayi min yankan, kuma bazanga dabban ba yayin da'ake yankata.

MAI BADA AMSA: Prof. Dr. Sa'ud bn Abdullah Alfunaisan. Tsohon shugaban Faculty of Shari'ah, Imam Muhammad Bn Sa'ud University Riyadh.

RANA: 05-12-1428 A.H.

AMSA:Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Tsira da Aminci su Kara tabbata ga Manzan Allah. Bayan Haka: Ya Halarta ka wakilta Kawun ka dayake wani gari da kabashi kudin yasaya kuma yayi maka yanka, saboda ita dai Layya, sunna ce me karfi, wasu kuma sukace wajibi ce ga wanda yake da hali, kuma kallon yankan da kuma cin naman abin layyan, sunna ce ba wajibi ba, musamman kuma tunda Iyalanka zasu yi layyan, kuma abin layya guda daya yana isarma mutum da iyalan gidansa koda suna da yawa, kuma kamar yadda ka bayi bayanin halin da kawunka yake ciki wato yafi iyalanka bukata, saboda haka inka bashi kudin layyan yana wata kasa yayi maka, yahalarta a cikin Shari'a. Allah shine mafi sani.

Menene Hukuncin Tabarruki (Neman Albarka)

Tambaya:
Menene Hukuncin Tabarruki (Neman Albarka)
da duk wani abu da yashafi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a Lokacin dayake da rai, da bayan mutuwarsa, da tabarrukin da Sahabbai sukayi da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin rayuwarsa, kuma shin hakan ya tabbata a bayan rasuwarsa? kuma naji cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yaba wani bargonsa, kuma a binne wani dashi a bayan mutuwarsa? kuma shin yatabata cewa Abdullahi dan Umar yayi tabarruki da mimbarin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam? kuma meye ra'ayinku gameda wanda yake cewa yanada gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam?.
Malami da ya amsa:
Ustaz Dr. Khalid almushaiqih
Rana: Alhamis 30 Rajab 1427 A.H
Lambar Fatawa: 16619.
Daga: shafin www.almoslim.net
AMSA:
Dukkan yabo da godiya sun tabata ga Allah Mahaliccin Bayi, tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabansa gabaki daya. bayan haka:
Yin Tabarruki da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin da yake da rai, ya kunshi nau'i guda biyu na Albarka, Albarka tashi da kansa da Albarka ta ma'ana.
Amma neman albarka tashi ta kansa: To Sahabai Allah yakara Yarda agaresu, sun kasance suna yin tabarruki da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, saboda Allah Subhanahu Wata'ala yasanya albarka agaresa, kamar yanda hakan yazo a cikin Hadisin Bukhari da Muslim da waninsu, cewa sunayin tabarruki da Gashinsa da Yawunsa da kakinsa da guminsa da tufafinsa da sauransu.
Nau'i na biyu kuma shine: yin Tabarruki na Ma'ana, Annabai Sallallahu Alaihi Wasalllam, Shine mafi girman dalili ko sababi ga al'ummarsa na samun Albarka ta hanyar karantarda su da shiryar dasu da fitar dasu daga duhu zuwa gas haske. to amma bayan wafatinsa, to Albarka ta ma'ana ta yanke, sedai abinda aka ruwaito daga wasu daga cikin Sahabbai Allah yakara masu yarda, cewa sun kasance sun kiyaye wasu daga cikin abubuwa na Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kuma sunayin Tabarruki dasu kamar yadda yazo a cikin Sahih Abukhari, daga Ummu Salamah Allah yakara yarda agareta, tanada abun wuya na azurfa ta kiyaye gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a ciki, to irin wadannan alamomi ko abubuwa, sahabbai sun kasance, sun kiyiyesu. To amma a Yau: irin abinda shuwagabannin Sufaye suke ik'irari da y'an damfara na cewa sunanan da wani sashi na gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ko tufafinsa ko makamancin haka, duk k'arerayine da basu da wata kamshin gaskiya, saboda basu da wani dalili -wato hujja akan hakan- ingantatta a cikin Shari'a ta sanadi, to saboda haka babu wani abinda yarage face, Albarka ta ma'ana, ta neman Albarka da abubuwan daya fuskantar, da abubuwan dayayi umarni dasu da abubuwan dayayi hani dasu da tsayuwa akan Sunnarsa da nisantar Sab'a masa. kuma ga Allah muke neman dacewa.

Menene Ma'anar Mafarki kuma Yaya Yake?

Daga Shafin: www.islamtoday.net/question

Mai Amsa Tambaya:

Al-allamah Abdurrahman bn Abdullahi Al-ajlan Malami a haramin Makkah. Rana: 15-12-1422 A.H

Amsa:

Mafarki Shine mutum yagansa yanayin Jima'i da wata mace, to idan ya fitar da maniyyi a wannan lokaci to wanka ya wajaba akansa, idan kuma bai fitar da maniyyi ba, wankan bezama dole akansa ba, saboda fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam "Ruwa yana wajaba ne -wato yin wankan janaba- saboda fitar ruwa -wato maniyyi" Muslim ya ruwaitoshi lambar hadisi na 343 daga hadisin Abu Sa'idil Khuduri Allah yakara masa Yarda.

Bam - Bamci tsakanin Wankan Janaba da Wankan tsabta

DAGA: Shafin: www.islamtoday.net

Tanbaya:

Menene Bambanci tsakanin Wankan Janaba da Wankan tsabta? wajen isarwarsu daga alwala ko rashinta? kuma shin yin Alwala sharadi ne game da wankan tsabta? dakuma wajen yin niyya, Allah yasaka maku da Alkhairi.

Mai Me bada Amsa:

Dr. Sulaiman bin Wa'il Attuwaijiri, Mamba a kwamitin malamai na Jami'ar Ummul Qura dake makkah.

Rana: 27-6-1424 A.H.

Amsa: Wankan Janaba, wankane dayake dauke Hadasi babba, ita kuma Alwala tana dauke hadasi ne wanda yake karami, shi kuma wanka na tsabta, ba ya dauke wani hadasi, to da mutum zeyi niyyan wanka, wato bana janaba ba, kawai yayi wankan tsabta ne ko wankan juma'a, se yayi nufin dauke hadasi karami dashi wato alwala, to be isar masa ba, domin a wankan babu nufin dauke hadasi a cikinsa, Allah madaukakin Sarki kuma yana cewa "kuma idan kun kasance masu janaba to kuyi tsarki" to alwala tana shiga cikin wankan janaba wajen dauke hadasi, se hadasi karani ya shiga cikin hadasi babba, wajen daukewa da abinda ze halarta sallah, amma shi kuma wanka na tsabta, badauke hadasi yakeyi ba saboda haka be idarwa gameda alwala, myazama dole yayi alwala da farillanta da jerantawa a gabbai. Allah shine mafi sani.